Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a shirin ta na “Operation Kukan Kura” inda ta kama masu aikata laifuka daban-daban tare da kwato kayayyakin da aka sace ko aka yi safarar su.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta cimma wannan nasara cikin kasa da wata guda.
Adadin abubuwan da aka kama:
‘Yan daba: 57
Masu safarar kwayoyi: 8
Masu safarar mota: 9
‘Yan fashi da makami: 17
Barayi: 9
Ababen hawa da dabbobi:
Motoci: 5
Babura: 13
Shanu: 3
Adaidaita sahu: 2
Makamai da miyagun kwayoyi:
Bindigu, adduna da makamai kirar gida: 169
Tramadol mai darajar kudi ₦60,300,000
Kwalaye 6 na Pregabalin mai kimar ₦22,425,000
Wiwi (ƙunshi 523)
POS guda 5
Da sauran kwayoyi da kayan sata
Kwamishinan ya ce wannan nasara ta nuna jajircewar rundunar wajen yaki da aikata laifi a jihar Kano. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai da bayar da bayanai don tabbatar da tsaro.
Ya ƙara da cewa dukkan miyagun kwayoyin da aka kama za a mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen Kano don ci gaba da bincike da daukar mataki.


