Nan da shekaru 4 masu zuwa za’a daina maganar rashin tsaro a Najeriya–Abbas

0
40

Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya cikin shekaru hudu masu zuwa.

Ya bayyana haka ne a wani taro da aka shirya a Abuja, inda ya ce gwamnati na aiki tukuru wajen aiwatar da matakai na musamman domin samar da yanayi mai kyau da zai magance ta’addanci da satar mutane.

Abbas ya kara da cewa majalisar dokoki tare da shugaban kasa sun tanadi karin kasafin kudi musamman ga bangaren ilimi da kiwon lafiya, tare da sabbin tsare-tsaren haraji da za su bunkasa tattalin arzikin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here