Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027– Jerry Gana

0
73

Tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Gana ya ce, bayan shekaru 10 da saukarsa daga mulki, ’yan Najeriya suna son dawowar Jonathan saboda sun gwada sauran shugabanni kuma sun ga bambanci.

A cewar Gana, “zan tabbatar muku cewa Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 kuma mun shirya kada masa ƙuri’a don dawowar sa fadar shugaban ƙasa.”

Jonathan ya sha kaye a hannun tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a 2015, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin PDP bayan shekaru 16 a kan karaga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here