Jami’in ɗan sanda ya rasa ransa sakamakon harbin kansa a Kano

0
97

Wani jami’in ƴan sanda a Kano mai suna Aminu Ibrahim ya rasu bayan da bindigarsa ta harba a bisa kuskure a bakin aiki.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:40 na safiyar Asabar a unguwar Hotoro, kamar yadda rahotanni daga kafar yada labarai ta mai sharhi akan al’amuran tsaro Zagazola Makama suka bayyana.

Shaidu sun ce Ibrahim, wanda ke aiki da rundunar ƴan sandan Kano, ya shiga bandaki a harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, inda aka ji ƙarar harbin bindiga.

Binciken farko ya nuna cewa yayin da yake tsugunne, bindigar AK-47 ɗinsa da ke rataye a wuyansa ta tashi, lamarin da ya jawo mummunan rauni a kansa.

An garzaya da shi zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa. Rahoton ya ce an samu bindigar tare da harsashi guda ɗaya da aka harba daga cikin 30 da aka ba shi, inda aka lissafa sauran 29.

Gawarsa na cikin dakin ajiye gawa, inda ake shirin gudanar da binciken gano musabbabin mutuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here