Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun zagayowar ranar samun yancin kai
Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta sanar da cewa ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za ta kasance hutun ƙasa domin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Ya kuma taya ’yan Najeriya murnar wannan rana mai tarihi, yana mai kira da a ci gaba da zama masu kishin ƙasa da haɗin kai domin cigaban al’umma.
Wannan sanarwa ta tabbatar da cewa dukkan ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu za su yi hutu a wannan rana, yayin da ake gudanar da bukukuwan bikin ’yancin kai a sassa daban-daban na ƙasar nan.


