Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shirya wani taron kwanaki biyu a Abuja domin tattauna hanyoyin magance talauci da habaka tattalin arzikin yankin.
Taron, wanda zai fara a yau Litinin, zai kuma kasance dandalin nuna albarkatun ma’adinai da ake da su a yankin arewa da nufin jawo hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddare, ya ce taron zai yi nazari kan damarmakin noma da ma’adinai da kuma yadda za a iya sarrafa su domin samar da ayyukan yi.
Ya bayyana cewa duk da cewa kashi 75% na ƙasar noma a Najeriya na arewa, yawancin matasan yankin na fama da rashin aiki. A cewarsa, taron zai zama wata hanya ta jawo hankalin masu saka jari wajen kafa masana’antu da amfani da albarkatun da ake da su.
NEF ta ce an gayyaci gwamnonin arewa 14 da jami’an babban birnin tarayya domin halartar taron, tare da fatan za a samar da hanyoyin da za su taimaka wajen fitar da yankin daga kangin talauci da rashin ci gaba.