Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sanar da baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 domin magance matsalolin da suka daɗe suna damun mambobin ta.
Shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana haka a Abuja, inda ya yi gargadin cewa idan gwamnati ta gaza aiwatar da bukatun nan da lokacin da suka bayar, ASUU za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu. Ya kara da cewa idan har ba a sami maslaha ba, hakan na iya rikidewa zuwa cikakken yajin aikin da ba shi da iyaka.
Daga cikin manyan bukatun ASUU akwai sake tattaunawa kan yarjejeniyar shekarar 2009, sakin kudaden farfado da jami’o’i, biyan bashin albashi, da kuma samar da ingantaccen tsarin daukar nauyin ilimin jami’a a Najeriya.
A martanin da ta bayar, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kafa kwamitin karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba bukatun kungiyar tare da fitar da shawarwari. Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon aikin kwamitin, lamarin da ya bar makomar tattaunawar cikin rashin tabbas.


