Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kano reshen wakilan kafafen yaɗa labarai (Correspondents Chapel) ta gudanar da taron musamman na “Taron Shan Shayi” a cibiyar ƴan jaridu ta ƙasa NUJ, a ranar Lahadi, inda ta gayyaci Farfesa Sule Yau Sule a matsayin bako na musamman.
Taron ya haɗa ‘yan jarida, shugabanni a fannin yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin musayar ra’ayoyi da ƙarfafa zumunci.
Shugaban ƙungiyar, Murtala Adewale, ya ce manufar shirin ita ce gina haɗin kai da kuma samar da dandalin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar jarida.
Farfesa Sule, wanda ya dauki nauyin wannan zama na musamman, ya yaba da shirin tare da kira ga ‘yan jarida su ƙara haɗin kai da tsayawa tsayin daka wajen kare martabar aikin jarida. Ya ce, “Aikin jarida shi ne ginshikin dimokuraɗiyya, dole a ci gaba da bayar da sahihan rahotanni a wannan zamani na yaɗuwar labaran ƙarya.”
Haka zalika, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Baba Halilu Dantiye, ya jaddada muhimmancin koyarwa da jagoranci ga matasan ‘yan jarida.
Shugaban NUJ Kano, Comrade Sulaiman Dederi, wanda mataimakinsa Mustapha Gambo ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin abin da ke ƙarfafa haɗin kai da tattaunawa tsakanin mambobi.
Manyan baki daga hukumomin tsaro, tsoffin shugabannin ƙungiyar da kuma masu yada labarai a Kano sun halarta, tare da yin kira ga ci gaba da irin wannan taro domin bunƙasa aikin jarida.