Jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki bada jimawa ba–NRC

0
23

Jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki–NRC

Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da kammala gyare-gyare a hanyar jirgin kasa na Abuja–Kaduna, wacce aka dakatar da jigila bayan hatsarin da ya auku a ranar 26 ga watan Agusta, inda mutane da dama suka ji raunuka.

Mai magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu, ya bayyana cewa an yi aikin cikin tsanaki don tabbatar da inganci da tsaro ga fasinjoji. Ya ƙara da cewa hukumar ta riga ta mayar da kuɗin tikiti ga fasinjoji 512 da hatsarin ya rutsa da su, tare da shirye-shiryen biyan sauran.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ranar da za a koma jigila ba, tana mai cewa a cikin ‘yan kwanaki kaɗan za ta fitar da cikakken jadawalin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here