Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga dukkan jami’an gwamnati da su kasance masu gaskiya da rikon amana, tare da gujewa duk wani nau’i na cin hanci da rashawa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin rufe taron bita na kwanaki uku da aka shirya wa kwamishinoni, mashawarta na musamman, da shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Kano a Kaduna.
Gwamnan ya ce manufar taron ita ce kara inganta nagartar shugabanci da kuma ilimantar da jami’an gwamnati kan rawar da ya kamata su taka wajen gudanar da amanar da aka dora musu.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa a kowane mataki ba, inda ya bukaci duk jami’an gwamnati su tabbatar da gaskiya a harkokin aiki.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamrad Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya idanu a ma’aikatu da hukumomi domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da ayyuka.
Malamai daga Jami’ar Bayero, Dr. Aminu Gusau da Dr. Muhammad Auwal Harun, ne suka gabatar da makaloli kan shugabanci nagari da kuma yaki da cin hanci da rashawa a wajen taron.