Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Sunayen Sabbin Kwamishinoni Ga Majalisa

0
12

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tabbatar da su a matsayin kwamishinoni.

Sunayen sun hada da Barr. Abdulkarim Kabir Maude, SAN, lauya mai gogewa da ilimi daga ABU Zaria, BUK da makarantu na waje, wanda ya shafe sama da shekaru 10 a aikin lauya.

Na biyu kuwa shi ne Dr. Aliyu Isa Aliyu, malami a fannin lissafi, tsohon malami a FUD da North West University, kuma Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Kano.

A wani bangare, gwamna ya kuma nada Barr. Salisu Muhammad Tahir a matsayin Babban Sakataren na Ma’aikatar Shari’a.

Gwamna Yusuf ya ce nade-naden na nuni da jajircewar gwamnatinsa wajen inganta nagarta, kwarewa da gaskiya a cikin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here