Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi mai shekaru 19 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da kimar su ta kai Naira miliyan 82.7.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce an cafke wanda ake zargin ne sakamakon sahihin bayani da ‘yan sanda suka samu.
A cewar Kiyawa, a ranar 20 ga Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 1 na rana, rundunar ta samu rahoto game da wata mota da ake zargin tana ɗauke da kwalaye cike da kwayoyi a unguwar Rimin Auzinawa, Kano.
“Daga nan aka bibiyi motar, aka kai farmaki gidan da aka ajiye ta, kuma aka kama wani matashi mai suna Usman Umar, ɗan shekara 19 da ke zaune a gidan,” in ji sanarwar.
Bincike a gidan ya kai ga gano:
603 fakiti na kwayar Tramadol (kimanin kwayoyi 60,300) – darajar su ta kai N60,300,000
299 fakiti na Pregabalin (kimanin kwayoyi 44,850) – darajar su ta kai N22,425,000
Jimillar kudin darajar kwayoyin ya kai N82,725,000.
SP Kiyawa ya ce matashin na taimaka wa jami’an tsaro wajen gano sauran ‘yan kungiyar da ke da hannu a safarar.