PENGASSAN Ta Dakatar Da Tura Ɗanyen Mai Ga Matatar Dangote

0
22

Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta ba da umarni ga mambobinta da su dakatar da tura gas da ɗanyen man fetur zuwa Matatar Fetur ta Dangote. Wannan mataki ya samo asali ne daga rikicin da ya taso kan korar ma’aikatan Dangote da suka shiga ƙungiyar.

Sakataren PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, ya bayyana cewa shugabancin masana’antar na zaluntar ma’aikata saboda sun yi amfani da ‘yancin haɗuwa da ƙungiya da kundin tsarin mulki ya ba su.

Ƙungiyar ta yi ƙarar cewa akwai rashin kayan kariya, rashin kulawa da walwala, wariyar albashi, da kuma rinjayen ƙwararrun ƙetare a manyan mukamai.

Sai dai masana’antar Dangote ta musanta zargin, tana cewa sauye-sauyen da aka yi na cikin gida ne domin inganta aiki, sannan ma’aikatan Najeriya sama da 3,000 na ci gaba da aiki a wajen.

PENGASSAN ta yi gargaɗi cewa idan ba a warware rikicin ba, hakan na iya barazana ga tsarin samar da makamashi da tsaron tattalin arzikin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here