Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta PENGASSAN ta bayar da umarni ga mambobinta a ranar Asabar da su katse duk wata hanyar isar da gas zuwa kamfanin sarrafa mai na Dangote.
Gas na daga cikin muhimman makamashi da ke gudanar da wasu manyan injina a cikin kamfanin. A wasikar da kungiyar ta aika, an nemi shugabanninta su tabbatar da cewa an rufe dukkan hanyar da ke kai man fetur zuwa kamfanin, tare da dakatar da lodin jiragen ruwa da za su nufi wurin.
Matatar Dangote a martaninta, ta bayyana wannan mataki da PENGASSAN ta ɗauka a matsayin wanda yake ba bisa ƙa’ida ba, tare da gargadin kungiyar da ta yi aiki cikin bin dokokin ƙasa.
Wannan rikici ya kara zurfafa takaddama tsakanin kamfanin Dangote da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar mai a ƙasar.