Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule, Kano, ta sanar da cewa ta daina karɓar dalibai a shirin NCE (Nigeria Certificate in Education), bayan amincewar Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da ta ba wa jami’ar izini ta fara shirin digirin B.Ed (Bachelor of Education).
Wannan ci gaban na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren harkokin ilmi na jami’ar, Alhaji Auwalu Mudi Yakasai, ya rattaba wa hannu a madadin maga takardan jami’ar wacce aka aikawa jami’ar da kuma jama’a.
Sanarwar ta bayyana cewa:
> “Da amincewar da NUC ta bayar don fara shirin digiri na B.Ed, shiga shirin NCE ba zai sake yiwuwa ba. Saboda haka, duk masu neman NCE a jami’ar su gaggauta canja takardun neman shiga karatu ta dandalin JAMB zuwa B.Ed.”
Haka kuma, an umarci duk masu nema da su sayi Green Card a dandalin JAMB sannan su canja shirin daga NCE zuwa B.Ed, matuƙar sun cika sharuddan shiga, wanda ya haɗa da:
samun credits 5 a SSCE (tare da Ingilishi a matsayin tilas),
da kuma samun ammaki 150 a jarabawar JAMB.
Wannan matakin na nufin cewa daga yanzu, jami’ar za ta rika karɓar ɗalibai ne kawai zuwa matakin digiri a fannin ilimi.