Idan Kwankwaso ya dawo APC zamu karɓe shi a matsayin mahaukaci–Ganduje

0
22

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa idan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magoya bayansa suka dawo cikin APC, za a karɓe su ne a matsayin “mahaukata da suka lashe abin da suka taɓa faɗa.”

Ganduje ya yi wannan magana ne yayin wani taron shugabannin jam’iyyar APC a Kano ranar Alhamis, inda ya yi watsi da jita-jitar cewa Kwankwaso na shirin dawowa cikin jam’iyyar.

A cewarsa, Kwankwaso ya taɓa yi wa APC ba’a, har ya ce “sai mahaukaci ne kawai zai shiga jam’iyyar APC.” Ya kuma ƙara da cewa yanzu da ake rade-radin dawowar sa, idan hakan ta faru za a karɓe shi bisa wannan furuci nasa.

Game da yiwuwar sulhu tsakaninsa da Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, Ganduje ya ce hakan ba abin mamaki ba ne, domin suna da kwarewar mulki da za ta iya taimaka wa gwamnatin yanzu idan haɗin kai ya zama dole.

Sai dai ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da rashin shugabanci mai tsari, yana cewa:

“Sun samu kuɗaɗe cikin watanni shida fiye da waɗanda gwamnatinmu ta samu a cikin shekaru takwas. Amma me suka yi da su? Wannan gwamnati bata da tsari.

Haka kuma, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Yusuf tana kashe kuɗaɗe a kan ayyuka marasa amfani, yana kiran ta “gwamnatin tsageru mai cike da rudani.”

Dangane da cire shi daga shugabancin APC na ƙasa, Ganduje ya ce lamarin tsarin rarraba madafun iko ne, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai yi masa laifi ba.

“Mulki na Allah ne, yana ba wanda ya so a lokacin da ya so,” in ji shi.

Ya ƙaryata rade-radin cewa APC na raguwa, inda ya jaddada cewa jam’iyyar na ci gaba da kasancewa babbar jam’iyya a Najeriya duk da wasu canje-canje na sauyin sheƙa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here