Hukumar NAHCON Ta Bayyana Farashin Aikin Hajji Na 2026

0
18

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta fitar da sabbin kudaden aikin Hajjin shekarar 2026, inda aka samu raguwar farashi idan aka kwatanta da na 2025.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da BBC daga birnin Makka, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta amince da sabbin farashin ne bayan dogon nazari da kuma tattaunawa da hukumomin Saudiyya.

A cewar Farfesa Usman, an tsara farashin ne bisa shiyyoyi domin daidaita biyan kuɗin maniyyata:

Shiyyar Maiduguri/Yola (Yobe, Borno, Adamawa, Taraba): daga N8,327,000 a 2025 zuwa N8,118,000 a 2026. An samu ragi N208,000.

Sauran jihohin Arewa: daga N8,457,685 zuwa N8,244,000. An samu ragi N212,000.

Jihohin Kudu: daga N8,784,000 zuwa N8,561,000. An samu ragi N223,000.

Ya ce wannan raguwar da aka samu ta biyo bayan abubuwa biyu da suka shafi tsadar rayuwa a Saudiyya da kuma canjin ƙimar dala.

> “Mun samu sauƙi a kuɗin Misha’ir inda muka rage daga Riyal 4,770 zuwa Riyal 3,900 kowanne alhaji. Haka kuma ƙididdigar da muka yi a kan dala a bana ta fi ta bara sauƙi,” in ji shi.

Dangane da lokacin biyan kuɗi kuwa, NAHCON ta sanar da ranar 31 ga Disamba, 2025 a matsayin wa’adin ƙarshe ga duk maniyyatan da ke son halartar aikin Hajjin 2026. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here