Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur (PMS) da naira, lamarin da ya tayar da hankulan ‘yan kasuwa tare da haifar da damuwa kan farashin mai da matsin tattalin arzikin musayar kudi.
A wata sanarwa da kamfanin ya tura wa abokan cinikin sa da misalin ƙarfe 6:42 na yamma a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, bayan ƙarewar tsarin musayar mai da naira.
Sanarwar wacce Sashen Harkokin Kasuwanci na matatar Dangote ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa kwastomomin da ke da ciniki a kan naira za su iya neman a mayar musu da kuɗin su.
Kamfanin ya ce:
> “Mun riga mun wuce adadin man da aka ware mana ta tsarin siyan ɗanyen man fetur da Naira daga gwamnatin tarayya, saboda haka ba za mu iya ci gaba da sayar da Mai da naira ba.
Masana harkokin kasuwanci sun yi gargadin cewa sabon matakin na iya haifar da tashin farashin mai zuwa fiye da ₦900 kowanne lita, yayin da wasu suka nuna tsoron cewa hakan zai ƙara tsananta dogaro da dala a kasuwar mai.