Ɗaliban jihar Abia ne suka fi samun nasara a jarrabawar NECO ba na Kano ba–Rahoto 

0
42
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Wani rahoton jarabawar NECO SSCE na shekarar 2025, ya nuna cewa Jihar Abia ce ta fi kowace jiha nasara a sakamakon, jarrabawar ba Kano ba, kamar yadda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ikirari a shafinsa na sada zumunta.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa Kano ce ta zama ta farko a kasa, yana danganta hakan da gyare-gyaren ilimi da gwamnatinsa ta yi. Amma binciken da aka yi ya tabbatar da cewa ikirarin nasa ba haka ba ne.

Rahoton jaridar Premium Times, yace a hakikanin gaskiya, Abia ta samu kashi 83.31% na dalibanta sun ci jarabawa tare da samun ƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi. Sai Imo da Ebonyi da suka biyo baya da kaso 83.09% da 80.60%.

Kano kuwa, duk da cewa ita ce ta fi yawan ɗaliban da suka rubuta jarabawar sama da 136,000 – kashi 49.84% kacal ne suka ci, yayin da fiye da rabin daliban suka fadi. Wannan ya sanya Kano a mataki na 29 cikin jihohi 37 da suka shiga, wato daga cikin jihohin ƙarshe 10.

Jihohin da suka fi Kano a matsayi sun hada da Lagos (71.76%), Oyo (60.07%) da sauran jihohin kudu. Jihohin da suka yi kasa a sakamakon sune  Kano da Yobe, Adamawa, Plateau, Borno, Jigawa, Katsina, Zamfara da Sokoto.

Jimillar sakamakon NECO 2025:

Daliban da suka rubuta: 1,358,339

Wadanda suka ci biyar da Turanci da Lissafi: 818,492 (60.26%)

Mafi rinjayen jiha: Abia (83.31%)

Mafi kaskanci: Sokoto (35%)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here