Matatar mai ta Dangote ta sanar da korar dukkan ma’aikatan ta ƴan Najeriya, bisa ga abin da shugabancin kamfanin ya bayyana a matsayin “sabon tsarin gyaran aiki” a masana’antar.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan shiga ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN da mafi yawan ma’aikatan suka yi a kwanakin baya. Wata sanarwa da babban jami’in kula da ma’aikata, Femi Adekunle, ya rattaba wa hannu ta ce an samu laifin “tangarɗar aiki” a wasu sassa na masana’antar, lamarin da ya jawo korar ma’aikatan gaba ɗaya.
An umarci waɗanda abin ya shafa da su mika dukkan kayan kamfani da ke hannun su. Haka kuma, an shaida musu cewa za a biya su dukkan hakkokin sallama gwargwadon yarjejeniyar aikin da aka yi da su.
Shugabancin masana’antar ya kuma gode wa ma’aikatan da aka kora bisa gudunmawar da suka bayar kafin ɗaukar wannan mataki.
Wannan korar gaba ɗaya ta sake tayar da rikicin dake tsakanin matatar Dangote da ƙungiyoyin ma’aikata na masana’antar mai.