Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa babu gaskiya a rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta na cewa ya mika takardar neman shiga wata jam’iyyar siyasa.
A cikin wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar a shafin sa na Facebook, a safiyar yau Juma’a ya nemi jama’a su yi hattara da irin waɗannan jita-jita.
Sanarwar ta ce, duk wani bayani na gaskiya kan al’amuransa za a rika sanar da shi ne ta kafafen sadarwa sahihai da sauran kafafen yaɗa labarai.
Idan za’a iya tunawa a ƴan kwanakin nan an samu jita-jitar cewa Kwankwaso, ya miƙa wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, buƙatar shiga cikin jam’iyyar tare da bayyana sharuɗan sa na komawar.