Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Naira ta ƙara samun ƙarfi a kasuwar musayar kuɗi, inda darajar ta za iya kaiwa tsakanin N1,300/$1 zuwa N1,400/$1 kafin ƙarshen shekarar 2025.
Rabiu ya yi wannan hasashen ne bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa sun haifar da ɗa mai ido, musamman wajen taimaka wa ‘yan kasuwa su daina dogaro kacokan ga Babban Bankin Najeriya (CBN) don samun kuɗin waje.
A cewarsa, gyare-gyaren gwamnati suna samar da ginshiƙai na ci gaban tattalin arziki, kuma hakan zai amfanar da ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Game da hauhawar farashin kayayyaki, shugaban BUA ya bayyana cewa farashin abinci ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, yana mai ƙarfafa jama’a da su ƙara haƙuri domin ana sa ran za a samu ƙarin ragin farashin kayayyaki nan gaba.
Ya kuma kara da cewa, da zarar darajar Naira ta ci gaba da ƙaruwa, farashin siminti da sauran kayayyakin masana’antu ma zai ragu a ƙasar.
Shugaban BUA ya yabawa gwamnati da manufofin Babban Bankin Najeriya, yana mai cewa a da kamfanoni sukan yi dogon layi a CBN domin samun kuɗin waje, amma yanzu an samu sauƙi ta hanyar tsarin kasuwanci na zamani.