Za’a gurfanar da manyan jami’an ƴan sanda akan ƙaryar shekarun haihuwa

0
69

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce za ta gurfanar da wasu manyan jami’an da aka yi ritaya guda biyar a gaban kotu bisa zargin ƙirƙirar shekarun haihuwarsu na ƙarya domin tsawaita lokacin aikin su.

An shigar da ƙarar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda alkalin kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya sanya ranar 25 ga Satumba domin fara shari’ar.

Cikin waɗanda ake tuhuma akwai Idowu Owohunwa, tsohon mataimakin sufeton ‘yan sanda; Benneth Igwe da Ukachi Opara, tsoffin kwamishinonin ‘yan sanda; Obo Ukam Obo, tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda; da kuma Simon Lough, tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda.

Rahoton ya nuna cewa Owohunwa ya canza shekarun haihuwarsa a watan Disambar 2024, inda ya bayyana an haife shi a 1970 maimakon 1967. Haka kuma, an ce Igwe ya canza shekarunsa daga 1964 zuwa 1968 tare da samun rikice-rikice a takardun shigar sa aiki. Lough kuma ya fuskanci zargin cewa ya sauya shekarun haihuwarsa daga 1967 zuwa 1969 a shekarar 2022.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa wannan laifi ya saba wa dokokin aikin gwamnati, kuma ana iya hukunta shi a ƙarƙashin sassa daban-daban na kundin laifuka.

Sai dai dukkanin waɗanda ake tuhumar sun musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin na siyasa da kuma ƙage. Sun ce matsalar ta samo asali ne daga takardar ƙorafi da wata ƙungiyar matasa mai suna Integrity Youth Alliance ta shigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here