Ya kamata a bawa jami’an mu damar ɗaukar makamai–FRSC

0
53

Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), Shehu Mohammed, ya bayyana cewa bai ga wata hanya ta ingantacciyar aiwatar da dokokin hanya ba face a ɗauki matakin bai wa jami’ansa makamai.

Mohammed ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Arise, a ranar Alhamis, inda ya bayyana ƙalubalen da jami’an hukumar ke fuskanta wajen tsayar da manyan motocin kaya a kan tituna.

“Ina kuke son mutum huɗu kacal su tsaya a gaban manyan motoci masu ɗauke da fasinjoji da dabbobi a kai, su ce za su tsayar da ita? Ba zai yiwu ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, rashin “ƙarfi na tilasta bin doka” yana hana jami’an FRSC gudanar da aikinsu yadda ya kamata, musamman a kan manyan titunan ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here