Shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas, ya yi jawabi ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo daga Ramallah, bayan da gwamnatin Amurka ta Trump ta hana shi bizar shiga ƙasar.
A jawabinsa, Abbas ya jaddada cewa harin da Hamas ta kai Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba ba zai sa kungiyar ta ci gaba da taka rawa a Gaza bayan yaƙin ba.
> “Mun tabbatar kuma za mu ci gaba da sanar da cewa Zirin Gaza wani ɓangare ne na ƙasar Falasɗinu. Jagorancin kuma a shirye muke mu ɗauki nauyi game da lamarin tsaro a can. Hamas ba ta da wata rawa da za ta taka wajen jagoranci.”
Shugaban ya kuma zargi Isra’ila da kai farmakin kisan kiyashi a Gaza, tare da yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin, a saki waɗanda ake garkuwa da su, a kuma karɓe makaman Hamas.
Mahmoud Abbas, wanda mai shekaru 89, ana kallonsa a matsayin jagora da tasirinsa ya ragu, inda Amurka ke zarginsa da rashin yin allah-wadai da ta’addanci. Hakan ne ma ya sanya ta hana shi bizar shiga ƙasar.