Shugaban EFCC ya ziyarci fadar Shugaban ƙasa yayin da Tinubu ya gana da gwamnan riƙon jihar Rivers 

0
84
Ola Olukoyede

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ziyarci fadar Shugaban ƙasa a Abuja ranar Laraba.

Ziyarar ta zo ne a dai-dai lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (rtd).

Idan za a tuna, Tinubu ya naɗa Ibas a matsayin shugaban rikon ƙwarya a Rivers bayan rikicin siyasa da ya daɗe tsakanin tsohon gwamna Nyesom Wike da magajinsa Siminalayi Fubara. A sakamakon gaza warware rikicin, shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a ranar 18 ga Maris, lamarin da majalisar dokoki ta ƙasa ta amince da shi.

Sai dai bayan watanni shida, an kawo ƙarshen dokar ta-bacin, inda Fubara ya koma kan mulki yayin da Ibas ya bar ofis. Majalisar dokokin Rivers ta ce za ta gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen jihar a lokacin mulkin na ɗan rikon ƙwarya, musamman duba kan kuɗaɗen da suka kai N254.37bn da jihar ta samu daga FAAC tsakanin Maris da Agusta 2025.

Haka kuma, an ga Ministan Kuɗi kuma Babban Ministan Tattalin Arzikin Ƙasa, Wale Edun, a fadar shugaban ƙasa, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko ziyarar ta shafi al’amarin Rivers ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here