Najeriya ta cancanci kujerar din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya–Tinubu

0
80

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nanata bukatar bai wa Najeriya wakilci na dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC).

Tinubu ya yi wannan kira ne a jawabin da ya gabatar ta hannun Mataimakinsa, Kashim Shettima, a yayin taron tattaunawa na babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA) da ake gudanarwa a birnin New York.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, Shugaban Ƙasar ya bayyana muhimmancin sake fasalin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya domin tabbatar da adalci da wakilci mai inganci.

Tinubu ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here