A yau an gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a birnin tarayya Abuja.
Taron ya mayar da hankali kan bukatar ‘yan Najeriya su tashi tsaye wajen kalubalantar tsarin mulkin danniya da ADC tace ana gudanarwa, inda tace hakan na haifar da talauci da rashin tsaro a ƙasar nan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta ce tana ƙara himma wajen haɗa kan al’umma don samar da nagartaccen shugabanci mai cike da gaskiya da adalci.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai, Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal, Nasir El-Rufa’i, Farfesa Sheikh Isa Ibrahim Pantami, da sauran su.