Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga aiki

0
54

Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga aiki a kananan hukumomi da hukumomin ilimi na makarantun firamare, bayan rahoton tantancewar ma’aikata ya gano takardun bogi, ma’aikatan bogi da cin hanci daban-daban.

Gwamna Dikko Radda ya ce tantancewar ta haɗa ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin ma’aikata 46,380. 

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin jihar za ta iya adana kuɗi har naira miliyan 453.3 a kowane wata idan aka aiwatar da shawarwarin kwamitin.

Kwamitin ya kuma gano rashin gaskiya a takardun haihuwa, ɗaukar yara ƙanana aiki, samun karin girma na bogi, da kuma ma’aikata da ke ba da gurabensu ga wasu. Haka nan, an kwato naira miliyan 4.6 daga jami’ai da suka karɓi albashi sau biyu.

Shugaban kwamitin, Abdullahi A. Gagare, ya bayyana cewa sakataren ilimi na Zango LEA ya haɗa baki wajen ɗaukar ma’aikatan bogi 24, yana mai cewa wannan babban cin amanar jama’a ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here