Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje (OFR), ya kai ziyarar ban girma wurin tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Abdullahi Tijjani Muhammad, ATM Gwarzo a gidan sa a jiya Laraba.
A yayin ziyarar, mutanen biyu sun tattauna kan muhimman al’amura da dama da suka shafi ci gaban al’umma da siyasa. ATM Gwarzo ya bayyana cewa ziyarar ta ba su damar yin tattaunawa mai amfani kan batutuwa daban-daban, kamar yadda ya bayyana a shafin sa na Facebook.


