Cibiyar masu karatun Alƙur’ani ta Ƙasa ta bayyana cewa ba ta da hannu a cikin nadin da aka ce an yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Khadimul Qur’an.
Shugaban cibiyar, Goni Sunusi Abubakar, ya bayyana cewa wata ƙungiya ta bogi ce ta yi amfani da takardar cibiyar wajen ƙirƙirar wannan batu.
Cibiyar ta gargadi jama’a da malamai su yi watsi da ikirarin, tare da jaddada cewa jagoranci sahihi na cibiyar yana ƙarƙashin Goni Sunusi Abubakar da amintattun shugabannin ta na ƙasa.


