Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027, manufofin gwamnatinsa za su bai wa muradun al’ummar Yoruba muhimmanci na musamman.
Atiku ya ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa shugabancinsa zai bai wa Hausawa/Fulani damar mamaye sauran ƙabilu, musamman Yoruba.
A cewar sa: “’Ya na ɗaukar Yarabawa a matsayin iyalai na na kusa da kuma surukai. Saboda haka wannan babu gaskiya a cikin sa,” in ji shi cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya kara da cewa dangantakarsa ta aure da kuma zamantakewa da al’ummar Yoruba sun isa su tabbatar da cewa shugabancinsa ba zai kawo wariyar ƙabila ba.