An gudanar da jana’izar Dattawan da jikan su ya kashe su a Kano

0
80

An gudanar da jana’izar wasu dattawa biyu da aka hallaka a unguwar Ƙofar Dawanau da ke birnin Kano, bayan da jikansu mai suna Mutawakkilu, wanda ake fi sani da Tony, ya caka musu wuƙa har lahira.

Bayan kisan, rahotanni sun nuna cewa matashin ya yi ƙoƙarin tserewa, amma jami’an tsaro sun cafke shi cikin gaggawa.

Wani mazaunin unguwar, Auwalu Ayuba, ya bayyana cewa lamarin ya girgiza al’umma, musamman ganin yadda ake zargin matashin na ta’ammali da miyagun ƙwayoyi tun kafin faruwar abin.

Sai dai zuwa yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa ya aikata wannan ta’asa ba, yayin da jami’an tsaro ke cigaba da bincike a kan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here