Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Mutawakilu Ibrahim, mai shekara 30, bisa zargin kashe kakanninsa a unguwar Kofar Dawanau, Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025, lokacin da aka ce matashin ya samu sabani da kakanninsa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75, da matarsa Hadiza Tasidi mai shekara 65, kan batun abinci.
A cewar rundunar ’yan sanda, yayin takaddamar, mutumin ya dauki wuka ya caka musu a jiki har lahira. An garzaya da su zuwa Asibitin Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu. An mika gawarwakin ga ’yan uwa domin binne su bisa tsarin addinin Musulunci.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke wanda ake zargi, kuma ana kyautata zaton yana cikin maye lokacin da lamarin ya faru. Ya kara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci a mika binciken ga sashen SCID domin ci gaba da zurfafa bincike.
Ya tabbatar da cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.