Sheikh Dr. Saleh bin Humaid, ya zama babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya

0
66

Sheikh Dr. Saleh bin Humaid, ya zama babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya

Rahotanni daga Inside the Haramain sun tabbatar da cewa an nada Sheikh Dr. Saleh bin Humaid a matsayin sabon Babban mai bayar da fatawa na Masarautar Saudiyya tare da shugabancin Majalisar Manyan Malamai.

Wannan nadin ya fito ne daga Mai kula da Masallatan Haramain guda biyu, kuma fadar sarautar na shirin fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba.

Hakan ya biyo bayan rasuwar Sheikh Abdulaziz Al-Asheikh, a ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here