Murtala Sule Garo ya taya T. Gwarzo murnar cika shekaru 65 a duniya

0
33

Ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar (APC) a zaɓen 2023, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ministan gidaje, Engr. Abdullahi Tijjani Gwarzo murnar cika shekaru 65.

A cikin gaisuwar taya murna da ya fitar ranar Laraba, Garo ya bayyana T. Gwarzo a matsayin jagora nagari masanin siyasa, jajirtacce wanda rayuwarsa ke cike da tawali’u da kuma hidima ga al’ummar jihar Kano da Najeriya gaba daya.

Ya yaba wa T. Gwarzo bisa yadda yake tafiyar da rayuwarsa cikin hidimtawa al’umma tun daga tushe har zuwa lokacin da ya zama mataimakin gwamnan Kano da kuma lokacin da aka nada shi karamin ministan gidaje har zuwa yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here