Mahara sun yi sanadiyar mutuwar mai juna biyu a jihar Kwara

0
49

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kai hari a ƙaramar hukumar Patigi ta jihar Kwara, inda suka kashe wata mace mai ciki tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Rahotanni sun ce maharan sun sace akalla mutum takwas, tare da raunata wasu da dama a yayin harin da ya faru ranar Talata.

Wani ɗan sa-kai ya bayyana cewa harin ya biyo bayan artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindigar, bayan da suka sace shanu da yawa, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe aƙalla huɗu daga cikin maharan.

Shaidu sun ruwaito cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna harbe-harbe kafin zuwan jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here