Lauyoyin Kano Sun Miƙa Ƙorafi Kan Alhassan Ado Doguwa Zuwa Majalisun Ƙasa

0
82

Kungiyar Lauyoyi ‘Yan Asalin Jihar Kano, ta tura takardun ƙorafi zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai kan zargin tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai, Hon. Alasan Ado Doguwa, da hannu a kisan mutane a Tudun Wada yayin zaɓen 2023.

Kungiyar ta bayyana cewa lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da barin wasu da raunuka. Saboda haka, sun nemi Majalisar Ƙasa ta saka baki domin tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka ce abin ya shafa.

A cikin ƙorafin, kungiyar ta bukaci kwamitocin Shari’a, Rundunar ‘Yan Sanda da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam su shiga binciken tare da samar da adalci. Haka kuma, sun yi kira ga majalisun biyu da su shirya zaman jin ra’ayin jama’a ko kuma su nemi cikakken rahoto daga rundunar ‘yan sanda da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano.

Kungiyar ta jaddada cewa a tsarin mulkin dimokuraɗiyya, babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma barin wannan zargi ba tare da bincike mai zurfi ba zai iya lalata tsarin shari’a a ƙasar nan.

Takardar ƙorafin wacce Dr. Jafar Sadik ya sanya wa hannu a madadin kungiyar, ta zo ne bayan sun mika makamanciyar takarda ga Ma’aikatar Shari’a ta Kano tare da hotunan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Sun ce wannan mataki na nufin tabbatar da an dauki mataki kan zargin da ake yi.

Dr. Sadik ya ce kungiyar na fatan majalisun tarayya za su tabbatar da adalci ga jama’a da suka rasa ‘yan uwa da kuma waɗanda abin ya shafa kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here