Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta kuduri aniyar kammala biyan dukkan hakkokin ’yan fansho kafin shekarar 2027.
Yusuf ya bayyana haka ne a gidan gwamnatin Kano yayin kaddamar da biyan bashin fansho na naira biliyan 5 karo na biyar. Ya tabbatar da cewa babu wanda zai tashi daga wajen taron ba tare da ya ga kuɗinsa a wayarsa ta salula ba.
Gwamnan ya ce an dade ana tarawa tsoffin ma’aikata basussuka, lamarin da ya jefa da dama daga cikinsu cikin halin ƙuncin rayuwa, amma gwamnatinsa ta ɗauki matakin magance matsalar cikin gaggawa.
“Mun yi imani cewa duk wanda ya yi wa jihar mu hidima ya cancanci ya sami hakkinsa cikin sauƙi. Saboda haka, kafin ƙarshen wa’adinmu a 2027, babu wani mai fansho da zai rage da korafi a Kano,” in ji shi.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa kafin ya hau mulki, an bar masa bashin ’yan fansho da ya zarce naira biliyan 48, amma zuwa yanzu an riga an rage bashin zuwa naira biliyan 27.