Darajar naira ta ƙaru akan Dalar Amurka 

0
179
Farashin Dala zuwa naira
Farashin Dala zuwa naira

Darajar naira ta samu ɗan ƙaruwa bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya rage kuɗin ruwa da maki 50, inda ya sauka zuwa kashi 27 cikin 100.

Haka zalika, farashin ɗanyen mai ya ɗan tashi zuwa $67.82 a kowace ganga, wanda ya nuna ƙaruwa da santi 19 (kashi 0.3%).

A kasuwar hukuma, naira ta tsaya kan N1,487.36/$1 a ranar Talata, lamarin da ya nuna ƙarin darajar kashi 0.08 idan aka kwatanta da N1,488.60/$1 a baya, bisa bayanan da CBN ta fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here