Babu hannun Tinubu a matsalolin da a’lumma ke fuskanta–Dan Majalisa Gadgi

0
59

Dan majalisa mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam a Jihar Filato, Yusuf Gagdi, ya shawarci ‘yan Najeriya da su riƙa tambayar gwamnonin jihohi da kan yadda suke amfani da kuɗaɗen da ake tura musu daga gwamnatin tarayya.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV, Gagdi ya bayyana cewa tun bayan cire tallafin man fetur, adadin kuɗin da jihohi ke samu ya ninka fiye da sau uku.

> “Jihohin da ke karɓar kusan N4bn a baya yanzu suna samun tsakanin N10bn zuwa N14bn a kowane wata. Amma ba kowane gwamna bane yake nuna aikace-aikacen kuɗin yadda ya dace,” inji shi.

Ya ce ya kamata ‘yan majalisa da al’umma su daina zargin shugaba Bola Tinubu kawai, saboda shi ya riga ya cika alkawarin da ya ɗauka ta hanyar ƙara kudaden shiga ga jihohi.

Dangane da tsaro kuwa, Gagdi ya bayyana cewa mafi yawan hare-haren da ake yi a Jihar Filato na fitowa daga makwabtanta, inda ya nuna damuwa kan yadda dazuka suka zama mafaka ga ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here