Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mata biyu a jihar Nasarawa, ciki har da matar wani Fasto wadda ke shayar da jariri mai watanni uku, inda aka nemi fansar Naira miliyan 50 kafin a sake su. Matar ta bayyana halin wahala da take ciki a cikin dajin da aka ajiye ta, tana kuka kan yadda aka raba ta da jaririnta.
A wani lamari dabam kuma, a daren Litinin an sace wani ɗan majalisar dokoki na jihar Filato, Laven Jacob, a gidansa da ke Jos. Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce tana kan aikin ceto.
Haka zalika, wata kotun soja ta musamman ta yanke wa sojoji huɗu hukunci kan zargin sayar da makamai ga ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas. Sojoji uku an yanke musu hukuncin daurin rai da rai, yayin da aka yanke wa ɗaya hukuncin shekaru 15 a gidan yari. Kotun ta bayyana cewa aikinsu babban cin amana ne ga ƙasa da kuma rundunar soji.