Majalisar Dattawan Najeriya ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke cikin Suite 2.05 na ginin Majalisar a ranar Talata.
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Alabi Adedeji, wanda ya tabbatar da cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya za ta samu damar komawa ofishinta kafin zaman majalisar da za a ci gaba da shi a ranar 7 ga Oktoba, 2025.
A makon da ya gabata, Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa domin sanar da niyyarta ta komawa bakin aiki bayan kammala hukuncin dakatar da ita na watanni shida.
Da buɗe ofishinta, yanzu haka an ba ta damar shiga cikin harabar Majalisar kuma tana iya shiryawa don ci gaba da ayyukan dokoki a zauren majalisa.
Rahotanni sun nuna cewa buɗe ofishinta kafin ranar komawa zauren majalisar zai bai wa Natasha damar halartar zaman majalisar cikin shiri.