Kotun Soji ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga sojoji masu safarar makamai ga ƴan ta’adda

0
110

Wata kotun soji a Maiduguri, jihar Borno, ta yanke wa sojoji huɗu hukunci kan zargin sayar da makamai da harsasai ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban kotun, Brigadier Janar Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa daga cikin sojojin, uku za’a yi musu ɗaurin rai da rai, yayin da aka yanke wa ɗaya hukuncin shekara 15 a gidan yari.

Sojojin sun amsa aikata laifuka da suka haɗa da sata, safarar makamai da taimaka wa ƴan ta’adda, wanda hakan ya saba wa dokokin rundunar sojin Najeriya.

Kotun ta yi gargadin cewa irin wannan safara barazana ce ga tsaron ƙasa da kuma nasarar ayyukan soja. Janar Abdullahi ya ƙara da cewa laifukan sun wuce karya doka, domin sun ƙunshi cin amana da kuma durƙusar da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta lamunci irin wannan rashin ɗa’a ko halayen cin amana daga cikin jami’anta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here