Gwamnatin Kano ta ƙara kaimi wajen kafa Jami’ar Harkokin Noma a Kura

0
86

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ganin an tabbatar da kafa Jami’ar Harkokin Noma ta Tarayya a Karamar Hukumar Kura.

Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda shi ne Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, ya kai ziyara ƙaramar hukumar domin duba wajen da za’a gina jami’ar, ciki har da Babbar Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Kwana (GGSS Kura) da Cibiyar Bunkasa Kogunan Hadejia–Jama’are da ke Kura.

Wannan mataki ya biyo bayan kudirin da Sanata Rufa’i Sani Hanga ya gabatar a majalisar dattawa domin fadada damar ilimi da bincike a fannin noma a Kano da kasa baki ɗaya.

A yayin ziyarar, Gwarzo ya jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da mara baya ga duk wani shiri da zai inganta ilimi, samar da abinci da kuma ƙirƙirar ayyukan yi ga matasa.

Shugaban Karamar Hukumar Kura, Alhaji Rabi’u Abubakar Suleiman Babina, ya ce makarantar GGSS Kura ta cika dukkan sharuddan kafa jami’ar, yayin da Shugaban Kwamitin Samar da Jami’ar, Alhaji Shehu Na’allah, ya nuna cewa jama’ar yankin suna son a bar cibiyar Hadejia–Jama’are yadda take, saboda muhimmancinta ga manoma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here