Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tambayoyi kan harin da aka kai wa tawagarsa a Jihar Kebbi.
Malami ya bayyana cewa an gudanar da binciken cikin kwarewa da mutuntawa a ofishin DSS na Birnin Kebbi, inda ya kara da cewa zai ci gaba da bayar da hadin kai domin ganin an kammala binciken yadda ya kamata.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 1 ga Satumba 2025, wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hari kan tawagar Malami bayan dawowarsa daga ziyarar ta’aziyya, inda suka lalata motocin tawagar da raunata wasu daga cikin magoya bayansa.
Malami ya ce harin na da alaka da siyasa, duk da cewa jam’iyyar APC ta nesanta kanta daga lamarin.


