Babban Bankin Najeriya (CBN) na shirin sanar da rage kudin ruwa karo na farko tun bayan annobar COVID-19.
Rahotanni sun nuna cewa Hukumar Tsara Manufofin Kudi (MPC) ƙarƙashin jagorancin Gwamnan babban bankin ƙasa CBN Olayemi Cardoso za ta bayyana wannan mataki a yau Talata da ƙarfe 2 na rana.
Mujallar Bloomberg ta ruwaito cewa masana tattalin arziki guda biyar sun yi hasashen rage kudin ruwa da maki 50, wanda zai sauke shi daga 27.5% zuwa 27%.
Da hakan, Najeriya za ta bi sahun ƙasashen Afirka kamar Afrika ta Kudu, Masar da Aljeriya waɗanda suka fara rage kuɗin ruwan basussuka a cikin shekarar da ta gabata.