Masarautar Saudiyya ta sanar cewa Babban Limamin ƙasar kuma Shugaban Majalisar Manyan Malamai, Sheikh Abdulaziz Al-Asheikh, ya rasu.
An shirya gudanar da sallar jana’izarsa a masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a yau Talata.
Sheikh Abdulaziz Al-Asheikh ya hau wannan mukami tun a shekarar 1999, inda ya shafe sama da shekaru biyu da rabi yana jagorantar al’amuran addini a masarautar.
Ya kasance babban malamin addini mafi daraja a Saudiyya, wanda ke fassara dokokin Shari’a tare da bayar da fatawowi kan al’amuran shari’a da rayuwar yau da kullum.