Rundunar ‘Yan sandan Kano ta cafke Nasiru Shitu, mai shekara 33 daga Kofar Waika, bisa zargin damfarar jama’a, da sunan cewa shi jami’an ɗan sanda ne.
An kama shi a ranar 21 ga Satumba a Kofar Dawanau yayin da yake sanye da kayan ‘yan sanda na ƙarya. Bincike ya tabbatar cewa ba shi da alaƙa da rundunar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce za a gurfanar da shi a kotu, yayin da kwamishina CP Ibrahim Adamu Bakori ya bukaci jama’a su rika sanar da irin waɗannan lamura ga runduna ta lambar gaggawa 07038188127.