Ƴan Najeriya masu aikata cin hanci zasu rasa damar shiga ƙasar Amurka

0
73

Gwamnatin Amurka ta gargadi ‘yan siyasa da jami’an gwamnati masu hannu a rashawa a Najeriya cewa za su iya fuskantar takunkumin hana samun biza zuwa ƙasar, a wani yunƙuri na ƙarfafa gaskiya da ingantaccen shugabanci.

Wannan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda aka ce duk wanda aka samu da laifin rashawa, ko da mutum mai matsayi ne, ba zai tsira daga hukunci ba.

> “Yaƙi da rashawa ba shi da iyaka, kuma duk wanda ya aikata ba zai tsere daga ladabtarwa ba. Ko manyan mutane ne, za a iya hana su samun bizar shiga Amurka,” in ji sanarwar.

A baya, Amurka ta riga ta ɗauki irin wannan mataki kan wasu ‘yan Najeriya da ta ce sun yi ƙoƙarin lalata zaɓe da kuma tsari na dimokuraɗiyya.

Haka kuma, ofishin jakadancin ya nuna damuwa kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma yadda hakan ke ƙara yawaita rashin daidaito da raguwar amincewar jama’a ga shugabanni.

Masu sharhi na ganin cewa wannan gargadi na iya zama wata babbar barazana ga duk wanda ke amfani da mukaminsa wajen karkatar da kuɗin al’umma ko kuma lalata tsarin mulki a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here